قُلۡ مَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍ إِلَّا مَن شَآءَ أَن يَتَّخِذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلٗا ٥٧
Qul mā as'alukum 'alayhi min ajrin illā man shā'a an yattakhidha ilā rabbihī sabīlā
Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya1 zuwa ga Ubangijinsa."
Bayanan ƙasa
1 Bã na neman wata ijãra sabõda inã karanta muku Alƙur'ãni, ko, sabõda inã shiryar da ku, amma wanda ya so ya ciyar da dũkiyarsa dõmin Allah, to, shĩ kam bã ni hana shi, sai ya ciyar. Kuma mun sani Annabi ba ya cin sadaka. A kan haka ne waɗansu Malamai suka hana karɓar ijãraa kan karantar da Alƙur'ãni. Abin da yake Mu'utamadi ya halatta sabõda Hadĩsi, kumada sauƙaƙewa ga aikin yãɗa addĩnin Musulunci. Hukumci yanã canzawa da canzãwar hãli.