وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱسۡمَعُواْۖ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَعَصَيۡنَا وَأُشۡرِبُواْ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡعِجۡلَ بِكُفۡرِهِمۡۚ قُلۡ بِئۡسَمَا يَأۡمُرُكُم بِهِۦٓ إِيمَٰنُكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ ٩٣
Wa idh akhadhnā mīthāqakum warafa'nā fawqakumut-tūra khudhū mā ātaynākum biquwwatin wasma'ū qālū sami'nā wa'asaynā wa ushribū fī qulūbihimul-'ijla bikufrihim qul bi samā ya'murukum bihī īmānukum in kuntum mu'minīn
Kuma a lõkacin da Muka riƙi1 alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!"
Bayanan ƙasa
1 A lõkacin da aka bã su Attaura sai suka ƙi aiki da ita sai da aka ɓamɓari dutse aka ɗaukaka shi sama a kansu, idan ba su yi aiki da ita ba ya fãɗa kansu. Sai suka karɓa, sa'an nan daga bãya kuma suka warware dõmin haka Ya ce: "Suka ce: Mun jiya kuma mun ƙiya." Hãsali dai Yahũdu sun ƙi aiki da Littãfinsu, Attaura.