Surat Al-Baqarah, aya ta 92

2:92

۞ وَلَقَدۡ جَآءَكُم مُّوسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ ٩٢

Walaqad jā'akum mūsā bil-bayyināti thummat-takhadhtumul-'ijla mim ba'dihī wa antum zālimūn

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi1 (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.

Bayanan ƙasa

1 Riƙo A nan ma'anarsa bautawa; watau kõmãwa ga maraƙi da ibãda, ku bar Allah, bãyan Musa ya nuna muku ãyõyin Allah, yana ƙãra ƙaryata maganarku, ta cewa kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku kawai. Dã kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku, dã waɗannan abubuwa ba su auku ba daga gare ku.