Surat Al-Baqarah, aya ta 62

2:62

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلصَّٰبِـِٔينَ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ ٦٢

Innal-ladhīna āmanū walladhīna hādū wan-nasārā was-sābi'īna man āmana billāhi wal-yawmil-ākhiri wa'amila sālihan falahum ajruhum 'inda rabbihim walā khawfun 'alayhim walā hum yahzanūn

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba1, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.

Bayanan ƙasa

1 Waɗanda suka koma, watau Yahũdu, daga maganar Mũsa, "Mun kõma garesu" Sura ta 7 aya ta 156, kuma Makarkata, jama'a ce daga Lãrabãwa suka karkata daga addĩnin ubanninsu zuwa ga bauta wa malã'iku. A farkon Musulunci sunã cewa ga wanda ya musulunta, wai ya yi kama da su.