Surat Al-Baqarah, aya ta 222

2:222

وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡمَحِيضِۖ قُلۡ هُوَ أَذٗى فَٱعۡتَزِلُواْ ٱلنِّسَآءَ فِي ٱلۡمَحِيضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطۡهُرۡنَۖ فَإِذَا تَطَهَّرۡنَ فَأۡتُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَكُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلتَّوَّٰبِينَ وَيُحِبُّ ٱلۡمُتَطَهِّرِينَ ٢٢٢

Wayas'alūnaka 'anil-mahīdi qul huwa adhan fa'tazilun-nisā'a fil-mahīdi walā taqrabūhunna hattā yathurna fa idhā tatahharna fa tūhunna min haythu amarakumullāhu innallāha yuhibbut-tawwābīna wayuhibbul-mutatahhirīn

Kuma suna tambayar ka game da haila1 Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin hukuncin sãduwa da mãtan aure a lõkacin hailarsu; watau jima'i ya haramta a cikin haila kõ bãyan haila gabãnin ta yi wanka. Kõ da ta yi taimama tã yi salla duk da haka dai sai tã yi wanka sannan farjinta yake halatta ga mijinta. Amma anã iya mubãshara da rungumayya ko a cikin haila bãyan tã ɗaura gyauto, tã rũfe cĩbiya zuwa gwiwa.