Surat Al-Baqarah, aya ta 221

2:221

وَلَا تَنكِحُواْ ٱلۡمُشۡرِكَٰتِ حَتَّىٰ يُؤۡمِنَّۚ وَلَأَمَةٞ مُّؤۡمِنَةٌ خَيۡرٞ مِّن مُّشۡرِكَةٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡۗ وَلَا تُنكِحُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤۡمِنُواْۚ وَلَعَبۡدٞ مُّؤۡمِنٌ خَيۡرٞ مِّن مُّشۡرِكٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَكُمۡۗ أُوْلَٰٓئِكَ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلنَّارِۖ وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَى ٱلۡجَنَّةِ وَٱلۡمَغۡفِرَةِ بِإِذۡنِهِۦۖ وَيُبَيِّنُ ءَايَٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ ٢٢١

Walā tankihul-mushrikāti hattā yu'minna wala'amatum mu'minatun khayrum mim mushrikatin walaw a'jabatkum walā tunkihul-mushrikīna hattā yu'minū wala'abdum mu'minun khayrum mim mushrikin walaw a'jabakum ulā'ika yad'ūna ilan-nāri wallāhu yad'ū ilal-jannati wal-maghfirati bi idhnihī wayubayyinu āyātihī lin-nāsi la'allahum yatadhakkarūn

Kuma kada ku auri mãtã1 mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin irin maza da mãtan wani addini da bã zã a aure su ba sai sun musulunta, watau mushirikai, banda mãtan Mutãnen Littãfi, sũ kam anã auren 'ya'yansu tãre da kãfircinsu. Bã a auren wanda ya yi ridda daga addinin Musulunci.