Surat Al-Baqarah, aya ta 219

2:219

۞ يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡخَمۡرِ وَٱلۡمَيۡسِرِۖ قُلۡ فِيهِمَآ إِثۡمٞ كَبِيرٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَإِثۡمُهُمَآ أَكۡبَرُ مِن نَّفۡعِهِمَاۗ وَيَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَۖ قُلِ ٱلۡعَفۡوَۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَتَفَكَّرُونَ ٢١٩

Yas'alūnaka 'anil-khamri wal-maysiri qul fīhimā ithmun kabīrun wamanāfi'u lin-nāsi wa ithmuhumā akbaru min naf'ihimā wayas'alūnaka mādhā yunfiqūna qulil-'afwa kadhālika yubayyinullāhu lakumul-āyāti la'allakum tatafakkarūn

Suna tambayar ka game da giya da cãcã.1 Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage."2 Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin hukuncin cãca da giya da ciyarwa ta alhħri. Cãca da giya harãmun ne dõmin cũtarsu tã fi amfaninsu yawa, ana hukunci da abin da ya rinjãya. Ayõyin wata sura sun bayyana haramcin.

2 Abin da ya rage daga larũrarku da ta iyãlanku da wanda ciyar da shi yake wãjibi a kanku, saura shi ne afwu. Daga afwu ake sadakar taɗawwu'i.