۞ يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَهِلَّةِۖ قُلۡ هِيَ مَوَٰقِيتُ لِلنَّاسِ وَٱلۡحَجِّۗ وَلَيۡسَ ٱلۡبِرُّ بِأَن تَأۡتُواْ ٱلۡبُيُوتَ مِن ظُهُورِهَا وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنِ ٱتَّقَىٰۗ وَأۡتُواْ ٱلۡبُيُوتَ مِنۡ أَبۡوَٰبِهَاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ ١٨٩
Yas'alūnaka 'anil-ahillati qul hiya mawāqītu lin-nāsi wal-hajji walaysal-birru bi an ta'tul-buyūta min zuhūrihā walākinnal-birra manit-taqā wa tul-buyūta min abwābihā wattaqullāha la'allakum tuflihūn
Kuma suna tambayar ka1 daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara.
Bayanan ƙasa
1 Shiga Musulunci yarda ne da barin al'ãdu da hukunce-hukuncen jãhiliyya, sabõda haka ake sãmun tambayõyi da yawa daga sãbon Musulmi kãfin ya kammala da canza tsõfaffin al'ãdunsa da sãbabbi. Allah Yã yi tarbiyar Sahabban Annabi a cikin rãyuwar Annabi, bãyan saukar wahayi.