۞ هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَجَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا لِيَسۡكُنَ إِلَيۡهَاۖ فَلَمَّا تَغَشَّىٰهَا حَمَلَتۡ حَمۡلًا خَفِيفٗا فَمَرَّتۡ بِهِۦۖ فَلَمَّآ أَثۡقَلَت دَّعَوَا ٱللَّهَ رَبَّهُمَا لَئِنۡ ءَاتَيۡتَنَا صَٰلِحٗا لَّنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ ١٨٩
Huwal-ladhī khalaqakum min nafsin wāhidatin waja'ala minhā zawjahā liyaskuna ilayhā falammā taghasshāhā hamalat hamlan khafīfan famarrat bihī falammā athqalad da'awallāha rabbahumā la in ātaytanā sālihal lanakūnanna minash-shākirīn
Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare1 ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya."
Bayanan ƙasa
1 Asalin halitta, rai guda ce, watau Ãdam, Allah ya fitar da Hauwã'u daga Ãdamu, ya mayar da ita mãtarsa, daga gare su zũriya ta yaɗu, kuma ya zama sunnar rai, namijin ya natsu zuwa ga macen. Kuma daga nan zama ya ci gaba har idan mace ta yi ciki, bã ta damuwa da shi sai yã yi nauyi, ita da miji su dinga addu'a, sunã rõƙon Allah. A bãyan bukãtarsu tã biya sai su manta da Allah, su ɗõra jingina abũbuwa zuwa ga sabubbansu, su bar tunãnin Mai sabbabawa. Daga nan abu ya yi zurfi har ya kasance shirki; bauta wa wani tãre da Allah, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya.