Surat Al-A'raf, aya ta 169

7:169

فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٞ وَرِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَأۡخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا ٱلۡأَدۡنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغۡفَرُ لَنَا وَإِن يَأۡتِهِمۡ عَرَضٞ مِّثۡلُهُۥ يَأۡخُذُوهُۚ أَلَمۡ يُؤۡخَذۡ عَلَيۡهِم مِّيثَٰقُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن لَّا يَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِۗ وَٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ ١٦٩

Fakhalafa mim ba'dihim khalfun warithul-kitāba ya'khudhūna 'arada hādhal-adnā wayaqūlūna sayughfaru lanā wa in ya'tihim 'aradum mithluhū ya'khudhūhu alam yu'khadh 'alayhim mīthāqul-kitābi al lā yaqūlū 'alallāhi illal-haqqa wadarasū mā fīhi wad-dārul-ākhiratu khayrul lilladhīna yattaqūna afalā ta'qilūn

Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar1 wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?

Bayanan ƙasa

1 Sifar ƙasƙantacciya ita ce kãyan dũniya na haram, kamar rashawa. An kira ta sifa dõmin bã aba ce mai tsayuwa da kanta ba, kuma bã sifar abin kirki ba, sai dai abin da yake halaka ne nan da nan. Tãke gaskiya faɗa ne da Addini, watau yaƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya.