Surat Al-A'raf, aya ta 133

7:133

فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلۡجَرَادَ وَٱلۡقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَٰتٖ مُّفَصَّلَٰتٖ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ ١٣٣

Fa arsalnā 'alayhimut-tūfāna wal-jarāda wal-qummala wad-dafādi'a wad-dama āyātim mufassalātin fastakbarū wakānū qawmam mujrimīn

Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa1; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.

Bayanan ƙasa

1 Ãyõyin da suka je musu a cikin lõkatai daban-daban dõmin a ja hankalinsu, kõ zã su yi ĩmãni. Kõwace ãyã tanã kwãna bakwai sunã wahala da ita, sa'an nan su rõƙi Mũsã ya yi addu'a a kuranye ta, sa'an nan a bãyan wani lõkaci sai su kõma wa kãfircinsu, kamar yadda ãyõyi mãsu biyar wannan suka bayyana.