Surat Al-Anfal, aya ta 68

8:68

لَّوۡلَا كِتَٰبٞ مِّنَ ٱللَّهِ سَبَقَ لَمَسَّكُمۡ فِيمَآ أَخَذۡتُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ ٦٨

Llawlā kitābum minallāhi sabaqa lamassakum fīmā akhadhtum 'adhābun 'azīm

Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta,1 dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma.

Bayanan ƙasa

1 Abin da ya gabãta na Littãfi shi ne, amma Allah ne Masanin haƙĩƙa, abin da yake a cikin sũrar Ãl Imrãna, ãyã ta l59, inda aka bai wa Annabi umurnin ya yi shãwara da Sahabbansa ga abin da ya shãfi yãƙi, sa'an nan kuma ya dõgara ga Allah wajen zartar da abin da ya zãɓã daga shãwarar da suka bã shi.