Surat Al-Anfal, aya ta 57

8:57

فَإِمَّا تَثۡقَفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡحَرۡبِ فَشَرِّدۡ بِهِم مَّنۡ خَلۡفَهُمۡ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ ٥٧

Fa immā tathqafannahum fil-harbi fasharrid bihim man khalfahum la'allahum yaddhakkarūn

To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre1 waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa.

Bayanan ƙasa

1 Wãtau a kashe waɗanda aka kãma dõmin saura su gani su ji tsõro.