وَإِذۡ زَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَإِنِّي جَارٞ لَّكُمۡۖ فَلَمَّا تَرَآءَتِ ٱلۡفِئَتَانِ نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ وَقَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكُمۡ إِنِّيٓ أَرَىٰ مَا لَا تَرَوۡنَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَۚ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ ٤٨
Wa idh zayyana lahumush-shaytānu a'mālahum waqāla lā ghāliba lakumul-yawma minan-nāsi wa innī jārul lakum falammā tarā'atil-fi'atāni nakasa 'alā 'aqibayhi waqāla innī barī'um minkum innī arā mā lā tarawna innī akhāfullāha wallāhu shadīdul-'iqāb
Kuma a lõkacin da Shaiɗan1 ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."
Bayanan ƙasa
1 Shaiɗan ya fita zuwa ga Ƙuraishãwa a cikin sũrar surãƙ atu bn Mãlik, ya ce musu Yanã tãre da su, kuma shi ne maƙwabcinsu; watau danginsa, Kan'ãnãwa, bã zã su taɓã su ba da yãƙi, a lõkacin da suke yãƙi da Muhammadu. Bãyan haka da ya tafi Badar yã ga Malã'iku, shĩ ne ya kõma bãya, yanã c ewa wai shi yanã tsõron Allah; watau yanã yi wa Ƙuraishãwa izgili; sũ ne bã su tsõron Allah.