Surat Al-Anfal, aya ta 45

8:45

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمۡ فِئَةٗ فَٱثۡبُتُواْ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ ٤٥

Yā'ayyuhal-ladhīna āmanū idhā laqītum fi atan fathbutū wadhkurullāha kathīral la'allakum tuflihūn

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci1 Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.

Bayanan ƙasa

1 Ambaton Allah bayyane yã fi kyau a wurin yãƙi da wurin harama da hajji kõ umra, kuma da lõkacin da ake fitã zuwa ga masallacin ĩdi. Wurin da bã waɗannan wurãre uku ba, ambaton Allah, ya zama asirce yã fi kyau.