Surat Al-An'am, aya ta 125

6:125

فَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يَهۡدِيَهُۥ يَشۡرَحۡ صَدۡرَهُۥ لِلۡإِسۡلَٰمِۖ وَمَن يُرِدۡ أَن يُضِلَّهُۥ يَجۡعَلۡ صَدۡرَهُۥ ضَيِّقًا حَرَجٗا كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِي ٱلسَّمَآءِۚ كَذَٰلِكَ يَجۡعَلُ ٱللَّهُ ٱلرِّجۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ ١٢٥

Faman yuridillāhu an yahdiyahū yashrah sadrahū lil-islāmi waman yurid an yudillahū yaj'al sadrahū dayyiqan harajan ka annamā yassa''adu fis-samā'i kadhālika yaj'alullāhur-rijsa 'alal-ladhīna lā yu'minūn

Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa1 ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.

Bayanan ƙasa

1 Mai tãkãwa zuwa sama ƙirjinsa ƙunci yake yi, sabõda iskar numfashi tanã raguwa gare shi. Kuma shi yanã shasshekar gajiya da rashin iska. Wannan ilmi yanã a cikin mu'ujizar Alƙur'ani.