وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدۡقٗا وَعَدۡلٗاۚ لَّا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِهِۦۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ ١١٥
Watammat kalimatu rabbika sidqan wa'adlal lā mubaddila likalimātihī wahuwas-samī'ul-'alīm
Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya1 da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
Bayanan ƙasa
1 Musulunci kõ Alƙur'ãni ne cikon addinin Allah, babu mai iya zõwa da wani abu sãbo kõ ya ƙãra wani abu a cikin sa ta kõwace hanya kuma bãbu mai iya musanya wani abu a cikinsa. Ya cika ya kammala, sai biya kawai. Annabi ya ce: "Wanda ya yi wani aiki ba da umuruinsa a kan abin da ya aikata ɗin nan ba, to, an mayar masa; ba a karɓaba.".