Surat Al-Ahzab, aya ta 25

33:25

وَرَدَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِغَيۡظِهِمۡ لَمۡ يَنَالُواْ خَيۡرٗاۚ وَكَفَى ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلۡقِتَالَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ قَوِيًّا عَزِيزٗا ٢٥

Waraddallāhul-ladhīna kafarū bighayzihim lam yanālū khayran wakafallāhul-mu'minīnal-qitāla wakānallāhu qawiyyan 'azīzā

Kuma Allah Yã mayar 1da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi.

Bayanan ƙasa

1 Allah Yã kõre ƙungiyõyin kãfirai da iskarsa mai tsananin sanyi, watau iskar Saba.