Ramadan 2028
Ranar da ake tsammani
Jummaʼa 28 Janairu, 2028
1 Ramadan 1449 BH
Zuwa Jummaʼa 25 Faburairu, 2028
Kwanakin suna bin kalandar Ummul Qura ta Saudiyya. Inda ake fara wata da ganin jinjirin wata a gida, kwanan wata zai iya gaba ko baya da rana ɗaya.
Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Hijira, kuma watan azumin farilla. Musulmi suna azumi kowace rana daga alfijir zuwa faɗuwar rana na kwanaki 29 ko 30, kuma a cikinsa aka fara saukar da Alƙur'ani.
Daga Alƙur'ani da Sunna
- Yi azumi kowace rana ta watan, daga alfijir zuwa faɗuwar rana. (Alƙur'ani 2:183)
- Yi sallar dare (Tarawihi) da imani da neman lada. (Bukhari da Muslim)
- Ci sahur kafin alfijir, domin akwai albarka a cikinsa. (Bukhari da Muslim)
- Karanta Alƙur'ani kuma ka yawaita kyauta, kamar yadda Annabi ﷺ yake yi a Ramadan. (Bukhari da Muslim)
Hadisi
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ» Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.
عن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَسَحَّرُوا، فَإِنَّ فِي السَّحُورِ بَرَكَةً». Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ النَّاسِ، وَكَانَ أَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي رَمَضَانَ حِينَ يَلْقَاهُ جِبْرِيلُ، وَكَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ مِنْ رَمَضَانَ فَيُدَارِسُهُ القُرْآنَ، فَلَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدُ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ. Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne lokacin da Jibril ya haɗu da shi, ya kasance yana haɗuwa da shi a cikin kowane dare na Ramadan sai su yi nazaran shi AlƘu'ani, to Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta ta alheri daga iskar da aka aiko.
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi girman mutane a kyauta, ya kasance kyautarsa tana yawaita a cikin watan Ramadan lokacin da ya kasance yana bada abinda yake kamata ga wanda ya kamata, kuma sababi a cikin ƙaruwar kyautarsa abubuwane biyu: Na farko: Haɗuwarsa da Jibril - aminci ya tabbata agare shi -. Al'amari na ƙarshe: Karatun AlƘur'ani, shine karatu na zuciya. Sai nazarin da Jibril - aminci ya tabbata agare shi - yake yi da shi dukkan abinda ya sauka na AlƘur'ani ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta mafi yawan bayarwa kuma mafi aikata alheri, kuma mafi gaggawar anfanar da halitta daga iska mai daɗi wacce Allah Yake aikota da girgije da kuma rahama.
Duba kuma
Sauran shekaru
Sauran ranaku
Sabuwar Shekarar Hijira 2028Ashura 2028Isra'i da Mi'iraji 2028Daren Lailatul Qadri 2028Sallah Karama 2028Ranar Arafa 2028Babbar Sallah 2028 Kalandar Musulunci 1449 BH
Tambayoyi
Yaushe ne Ramadan 2028?
Ana sa ran Ramadan 2028 ya fara a ranar Jummaʼa 28 Janairu, 2028, wato 1 Ramadan 1449 BH a kalandar Ummul Qura.
Shin ranar Ramadan ta tabbata?
Ba ta tabbata ba sai an ga jinjirin wata. Ƙasashe da yawa suna sanar da farkon wata a daren da ya gabace shi, don haka ranar za ta iya canzawa da rana ɗaya.
Kwana nawa ne Ramadan?
Ramadan yana da kwanaki 29 ko 30. Yana ƙarewa idan aka ga jinjirin watan Shawwal, kuma Sallah Karama tana washegari.