Darasi 2 cikin 8
Wanene Allah?
Daga Alƙur'ani
قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ ﴿١﴾ ٱللَّهُ ٱلصَّمَدُ ﴿٢﴾ لَمۡ يَلِدۡ وَلَمۡ يُولَدۡ ﴿٣﴾ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ كُفُوًا أَحَدُۢ ﴿٤﴾
"Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci." "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata." "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba." "Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ ﴿٢٥٥﴾
Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.
فَاطِرُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ جَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَمِنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ أَزۡوَٰجٗا يَذۡرَؤُكُمۡ فِيهِۚ لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ ﴿١١﴾
(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasai, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ ﴿٢٢﴾ هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ ﴿٢٣﴾ هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ ﴿٢٤﴾
(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai. Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai tastãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi. Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa. Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.