Surat Yusuf, aya ta 15

12:15

فَلَمَّا ذَهَبُواْ بِهِۦ وَأَجۡمَعُوٓاْ أَن يَجۡعَلُوهُ فِي غَيَٰبَتِ ٱلۡجُبِّۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ لَتُنَبِّئَنَّهُم بِأَمۡرِهِمۡ هَٰذَا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ ١٥

Falammā dhahabū bihī wa ajma'ū an yaj'alūhu fī ghayābatil-jubbi wa awhaynā ilayhi latunabbi'annahum bi amrihim hādhā wahum lā yash'urūn

To, a lõkacin1 da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba."

Bayanan ƙasa

1 Suka cire rĩgarsa, suka jefa shi da gũga a cikin rĩjiya. Sa'an nan suka sanya wa rigarsa jinin wata dabba da suka yanka, dõmin ya zama alãmar cewa kerkeci ya cinye Yũsufu. Gã rĩgarsa ta ɓãci da jinin jikinsa, watau jinin shĩ ne alãmar yã mutu. Sai suka manta cewa kãfin kerkeci ya cinye yãro a cikin rĩgarsa, sai yã kekketa rĩgar tukun.