وَلَوۡ نَشَآءُ لَطَمَسۡنَا عَلَىٰٓ أَعۡيُنِهِمۡ فَٱسۡتَبَقُواْ ٱلصِّرَٰطَ فَأَنَّىٰ يُبۡصِرُونَ ٦٦
Walaw nashā'u latamasnā 'alā a'yunihim fastabaqus-sirāta fa annā yubsirūn
Dã Mun so, dã Mun shãfe gani 1daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?
Bayanan ƙasa
1 Dã Mun so shãfe ganinsu na ido kamar yadda Muka shãfe basĩrarsu ta hankali, dã Mun shãfe shi, sai su zama makãfin idãnu kamar yadda suke makãfin zũci. Sabõda haka ko sun so gani, bã zã su yi ba.