Surat Taha, aya ta 117

20:117

فَقُلۡنَا يَٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَٰذَا عَدُوّٞ لَّكَ وَلِزَوۡجِكَ فَلَا يُخۡرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلۡجَنَّةِ فَتَشۡقَىٰٓ ١١٧

Faqulnā yā'ādamu inna hādhā 'aduwwul laka walizawjika falā yukhrijannakumā minal-jannati fatashqā

Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi1 ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala."

Bayanan ƙasa

1 Anã farkar da ɗiyan Ãdamu ga maƙiyin ubansu wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa dũniya da haɗuwa da taklĩfi a cikinta. Kuma bin wannan taklĩfi yanã zame masa sauƙi idan sun bĩ shi yadda Allah Ya ce: amma idan sun bi hanyar Shaiɗan, maƙiyinsu, to, bãbu abin da zai sãmu a gare su fãce ƙãrin wahala daga dũniya har Lãhira.