Rabbi awzi'ni

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ إِحۡسَٰنًاۖ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ كُرۡهٗا وَوَضَعَتۡهُ كُرۡهٗاۖ وَحَمۡلُهُۥ وَفِصَٰلُهُۥ ثَلَٰثُونَ شَهۡرًاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَبَلَغَ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗ قَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَصۡلِحۡ لِي فِي ذُرِّيَّتِيٓۖ إِنِّي تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَإِنِّي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ ١٥

Wawassaynal-insāna biwālidayhi ihsānan hamalathu ummuhū kurhan wawada'athu kurhan wahamluhū wafisāluhū thalāthūna shahran hattā idhā balagha ashuddahū wabalagha arba'īna sanatan qāla rabbi awzi'nī an ashkura ni'matakal-latī an'amta 'alayya wa'alā wālidayya wa an a'mala sālihan tardāhu wa aslih lī fī dhurriyyatī innī tubtu ilayka wa innī minal-muslimīn

Kuma Mun yi wasiyya ga mutum1 game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."

Bayanan ƙasa

1 Mutum a cikin iyãlinsa, kõ ya zama mai gargaɗi ga kansa da nasĩha ga mahaifansa da zuriyarsa kamar yadda ya bayyana a cikin ãyõyi 13,l4 da l5, kõ kuma ya zama mai butulci ga kansa, ya tõzartar da iyãyensa da zuriyarsa, kamar yadda ya bayyanaa cikin ãyõyi 17 da 18.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Ahqaf gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Rabbi awzi'ni take a cikin Alƙur'ani?

Rabbi awzi'ni tana cikin Surat Al-Ahqaf, 46:15.