Surat Qaf, aya ta 30

50:30

يَوۡمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمۡتَلَأۡتِ وَتَقُولُ هَلۡ مِن مَّزِيدٖ ٣٠

Yawma naqūlu lijahannama halimtala'ti wataqūlu hal mim mazīd

Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,1 akwai wani ƙãri?"

Bayanan ƙasa

1 Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, "Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya." Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã neman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓawa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8.