Surat Maryam, aya ta 24

19:24

فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا ٢٤

Fanādāhā min tahtihā allā tahzanī qad ja'ala rabbuki tahtaki sariyyā

Sai (yãron da ta haifa) ya1 kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.

Bayanan ƙasa

1 Annabi Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya fãra magana ga uwarsa tun a lõkacin da aka haife shi yanã a ƙarƙashin uwarsa. Gudãnar ruwan marmaro a ƙarƙashinta da fitar da 'ya'yan dabĩno dagakututturen dabĩno, alãmu ne mãsu nũna cħwa Allah nã iya halitta jãrĩri bã da uba ba, kuma Yanã tãyar da matattu daga kabarinsu bã da wata wahala ba.