Laqad ja'akum rasulun

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

لَقَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولٞ مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ عَزِيزٌ عَلَيۡهِ مَا عَنِتُّمۡ حَرِيصٌ عَلَيۡكُم بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ ١٢٨

Laqad jā'akum rasūlum min anfusikum 'azīzun 'alayhi mā 'anittum harīsun 'alaykum bil-mu'minīna ra'ūfur rahīm

Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo1 daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin rahamar Allah game da aiko Manzõ daga cikin mutãne, cewa wata falala ce a gare su. Kuma shi Manzon nan ɗan'uwansu ne wanda bã ya son su da wani abu sai alheri, idan sun gãne dã sun bĩ shi, kuma idan ba su gãne bã, to, Allah Yã tsare shi daga sharrinsu, kuma Yã isar masa.

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَهُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ ١٢٩

Fa in tawallaw faqul hasbiyallāhu lā ilāha illā huwa 'alayhi tawakkaltu wahuwa rabbul-'arshil-'azīm

To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat At-Tawbah gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Laqad ja'akum rasulun take a cikin Alƙur'ani?

Laqad ja'akum rasulun tana cikin Surat At-Tawbah, 9:128-129.