Surat At-Tawbah, aya ta 52

9:52

قُلۡ هَلۡ تَرَبَّصُونَ بِنَآ إِلَّآ إِحۡدَى ٱلۡحُسۡنَيَيۡنِۖ وَنَحۡنُ نَتَرَبَّصُ بِكُمۡ أَن يُصِيبَكُمُ ٱللَّهُ بِعَذَابٖ مِّنۡ عِندِهِۦٓ أَوۡ بِأَيۡدِينَاۖ فَتَرَبَّصُوٓاْ إِنَّا مَعَكُم مُّتَرَبِّصُونَ ٥٢

Qul hal tarabbasūna binā illā ihdal-husnayayni wanahnu natarabbasu bikum an yusībakumullāhu bi'adhābim min 'indihī aw bi aydīnā fatarabbasū innā ma'akum mutarabbisūn

Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu1 mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."

Bayanan ƙasa

1 Ɗayan abũbuwa biyu mãsu kyau, sũ ne mutuwa a kan shahãda kõ rinjaya da sãmun ganĩma da izza.