۞ وَٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗا وَبِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡجَارِ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡجَارِ ٱلۡجُنُبِ وَٱلصَّاحِبِ بِٱلۡجَنۢبِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخۡتَالٗا فَخُورًا ٣٦
Wa'budullāha walā tushrikū bihī shay'an wabil-wālidayni ihsānan wabidhil-qurbā wal-yatāmā wal-masākīni wal-jāri dhil-qurbā wal-jāril-junubi was-sāhibi bil-jambi wabnis-sabīli wamā malakat aymānukum innallāha lā yuhibbu man kāna mukhtālan fakhūrā
Kuma ku bauta wa 1Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai tãƙama, mai yawan alfahari.
Bayanan ƙasa
1 Bauta wa Allah shi ne a bi umurninsa, a bar haninsa a kome. Sa'an nan ya biyar da nau'ukan mutane waɗanda mutum zai yi ihsani zuwa gare su gwargwadon darajarsu kuma da halinsa. Sa'an nan zargi a kan marowaci da sakamakonsa, da mai ciyarwa amma ba a bisa hanyar bauta wa Allah ba.