Surat An-Nahl, aya ta 98

16:98

فَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ ٩٨

Fa idhā qara'tal-qur'āna fasta'idh billāhi minash-shaytānir-rajīm

Sa'an nan idan ka karantã 1Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe.

Bayanan ƙasa

1 An yi saɓãni ga zaman Isti'ãza gabãnin karãtu kõ a bãyansa. Mãlik ya zãɓi a yi 'Isti'ãza' bãyan karãtu, kõ a bãyan an ƙãre yin salla, dõmin kada shaiɗan ya rinjãyi mutum a bãyan ĩmãninsa da salla. Sabõda haka ya karhanta shi a cikin salla. Wasu kuma sunã isti'ãzã a gabãnin karãtu kõ a gabãnin salla.