Surat An-Nahl, aya ta 56

16:56

وَيَجۡعَلُونَ لِمَا لَا يَعۡلَمُونَ نَصِيبٗا مِّمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡۗ تَٱللَّهِ لَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَفۡتَرُونَ ٥٦

Wayaj'alūna limā lā ya'lamūna nasībam mimmā razaqnāhum tallāhi latus'alunna 'ammā kuntum taftarūn

Kuma sunã sanya rabõ 1ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa.

Bayanan ƙasa

1 Sunã sanyãwar rabõ daga dabbõbi da hatsi ga gumãka kõ aljannu, alhãli ba su san amfãnin da gumãkan kõ aljannun suke iya jãwo musu ba kõ suke tunkuɗewa daga gare su. Akwai daga cikin ni'imõmin Allah, Ya shiryar da mutãne ga gãne cewa waɗannan gumãka da aljannu kõ wani mahalũƙi bã ya iya cũta kõ jãwo wani amfãni fãce da iznin Allah. Sabõda haka bãbu wanda ya cancanci a bauta masa fãce Allah, Mai tumɓuke cũta kuma Mai jãwo amfãni. Watau wannan bãyar da ni'imar 'yancin ɗan Adam kãmilan, su duka bãyi ne, bãbu daraja ga kõwa sai da taƙawa.Sanin haka wata ni'ima ce daga Allah.