يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعۡنَآ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ لَيُخۡرِجَنَّ ٱلۡأَعَزُّ مِنۡهَا ٱلۡأَذَلَّۚ وَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ وَلَٰكِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَا يَعۡلَمُونَ ٨
Yaqūlūna la ir raja'nā ilal-madīnati layukhrijannal-a'azzu minhal-adhalla walillāhil-'izzatu walirasūlihī walil-mu'minīna walākinnal-munāfiqīna lā ya'lamūn
Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma1 zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."
Bayanan ƙasa
1 Abdullah bn Ubayyi bn Salũl ya faɗi cewa "Wallahi idan mun kõma Madĩna wanda ya fi ƙarfi, lalle zai fitar da wanda ya fi ƙasƙanci." Yanã nufin Ansãrai mutãnen Madĩna zã su kõri Muhãjirai. Yã faɗi haka a cikin wata tafiya ta jihãdi. Aka gaya wa Annabi, sai ya yi musu. Allah Ya kunyata shi.