Surat Al-Ma'idah, aya ta 33

5:33

إِنَّمَا جَزَٰٓؤُاْ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓاْ أَوۡ يُصَلَّبُوٓاْ أَوۡ تُقَطَّعَ أَيۡدِيهِمۡ وَأَرۡجُلُهُم مِّنۡ خِلَٰفٍ أَوۡ يُنفَوۡاْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِۚ ذَٰلِكَ لَهُمۡ خِزۡيٞ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ ٣٣

Innamā jazā'ul-ladhīna yuhāribūnallāha warasūlahū wayas'awna fil-ardi fasādan an yuqattalū aw yusallabū aw tuqatta'a aydīhim wa arjuluhum min khilāfin aw yunfaw minal-ardi dhālika lahum khizyun fid-dunyā walahum fil-ākhirati 'adhābun 'azīm

Abin sani kawai sakamakon1 waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.

Bayanan ƙasa

1 Muhãrib shi ne ɗan fashi mai tare hanya da makamai. Ana yi masa ɗayan abin da aka ga yã dãce da shi. Wanda aka yi wa "Salbu" sai kuma a kashe shi. Amfanin Salbu shi ne a gan shi, dõmin hankalin mutãne ya natsu. Korewa yanzu sai ta koma ga ɗauri har ya mutu ko ya tuba.