وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُواْ ٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ يَنزَغُ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٗا مُّبِينٗا ٥٣
Waqul li'ibādī yaqūlul-latī hiya ahsanu innash-shaytāna yanzaghu baynahum innash-shaytāna kāna lil-insāni 'aduwwam mubīnā
Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma1 wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyanan ne.
Bayanan ƙasa
1 Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu.