وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَتُبَيِّنُنَّهُۥ لِلنَّاسِ وَلَا تَكۡتُمُونَهُۥ فَنَبَذُوهُ وَرَآءَ ظُهُورِهِمۡ وَٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَبِئۡسَ مَا يَشۡتَرُونَ ١٨٧
Wa idh akhadhallāhu mīthāqal-ladhīna ūtul-kitāba latubayyinunnahū lin-nāsi walā taktumūnahū fanabadhūhu warā'a zuhūrihim washtaraw bihī thamanan qalīlan fabi'sa mā yashtarūn
Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa1 Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye!
Bayanan ƙasa
1 A cikin wannan akwai gargaɗi ga mãlaman Musulmi, kada su shiga hanyar Yahũdu ta ɓõye ilmin gaskiya, ko kuwa abin da ya sãme su, sũ ma ya sãme su, kuma ya shiga da su mashigarsu. Wãjibi ne akan mãlamai su bãyar da abin da ke hannuwansu na ilmi mai amfãni, mai nũni a kan aikin ƙwarai, kada su ɓõye kõme daga gare shi. Idan sun ɓõye, to, la'anar Allah da malã'iku da ta mutãne zã ta tabbata a kansu, kamar yadda ta tabbata a kan mãlaman Yahũdu.