Surat Al-Fath, aya ta 24

48:24

وَهُوَ ٱلَّذِي كَفَّ أَيۡدِيَهُمۡ عَنكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ عَنۡهُم بِبَطۡنِ مَكَّةَ مِنۢ بَعۡدِ أَنۡ أَظۡفَرَكُمۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا ٢٤

Wahuwal-ladhī kaffa aydiyahum 'ankum wa aydiyakum 'anhum bibatni makkata mim ba'di an azfarakum 'alayhim wakānallāhu bimā ta'malūna basīrā

Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu 1daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.

Bayanan ƙasa

1 Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.