ٱلطَّلَٰقُ مَرَّتَانِۖ فَإِمۡسَاكُۢ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ تَسۡرِيحُۢ بِإِحۡسَٰنٖۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَأۡخُذُواْ مِمَّآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ شَيۡـًٔا إِلَّآ أَن يَخَافَآ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَا فِيمَا ٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَعۡتَدُوهَاۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ ٢٢٩
At-talāqu marratāni fa imsāku bima'rūfin aw tasrīhu bi ihsānin walā yahillu lakum an ta'khudhū mimmā ātaytumūhunna shay'an illā an yakhāfā allā yuqīmā hudūdallāhi fa in khiftum allā yuqīmā hudūdallāhi falā junāha 'alayhimā fīmaftadat bihī tilka hudūdullāhi falā ta'tadūhā waman yata'adda hudūdallāhi fa ulā'ika humuz-zālimūn
Saki sau biyu1 yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne Azzãlumai.
Bayanan ƙasa
1 Sakin aure da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da shi. Wanda ya saki matarsa sau ɗaya ko sau biyu, yanã iya mayar da ita kõ dã ba ta so ba matuƙar ba ta kãre idda ba. Wanda ya yi saki uku, bã ya iya kõma aurenta, sai tã yi jimã'i da wani sãbon miji a cikin aure sahĩhi. Sakin bãwa biyu ne.