Surat Al-A'raf, aya ta 60

7:60

قَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِهِۦٓ إِنَّا لَنَرَىٰكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ ٦٠

Qālal-mala'u min qawmihī innā lanarāka fī dalālim mubīn

Mashawarta1 daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya."

Bayanan ƙasa

1 Kissar Nũhu da mutãnensa tanã nũna yanda Annabawa mãsu kãwo gaskiya ke yin faɗa da miyãgun mutãne mãsu ƙin gaskiya, sunã ƙõƙarin rufe ta haka kuma ƙissõshin da ke tafe a bãyanta sunã nũna yadda ƙarya ke faɗa da gaskiya, ta hanyõyi dabam-dabam.