قَالَ ٱدۡخُلُواْ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ فِي ٱلنَّارِۖ كُلَّمَا دَخَلَتۡ أُمَّةٞ لَّعَنَتۡ أُخۡتَهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا ٱدَّارَكُواْ فِيهَا جَمِيعٗا قَالَتۡ أُخۡرَىٰهُمۡ لِأُولَىٰهُمۡ رَبَّنَا هَٰٓؤُلَآءِ أَضَلُّونَا فَـَٔاتِهِمۡ عَذَابٗا ضِعۡفٗا مِّنَ ٱلنَّارِۖ قَالَ لِكُلّٖ ضِعۡفٞ وَلَٰكِن لَّا تَعۡلَمُونَ ٣٨
Qāladkhulū fī umamin qad khalat min qablikum minal-jinni wal-insi fin-nāri kullamā dakhalat ummatul la'anat ukhtahā hattā idhad-dārakū fīhā jamī'an qālat ukhrāhum li ūlāhum rabbanā hā'ulā'i adallūnā fa'ātihim 'adhāban di'fam minan-nāri qāla likullin di'fun walākil lā ta'lamūn
Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane1 akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."
Bayanan ƙasa
1 Shũgabannin ɓata su ne ke fãra shiga wuta, sa'an nan mabiyansu, su shiga, dõmin shũgabanni sunã da laifi biyu; nãsu, na aikinsu, da kuma sababin da suka yi, na ɓatar da mabiyansu. Kuma an fahimta daga nan cewa, "Inã bin wane a kan ɓata, shĩ ne ya ɓatar da ni, bã ya zama hujja mai hana shiga wuta, dõmin AllahYã aza wa kõwane bãligi mai hankali da yayi binciken gaskiya gwargwadon iyãwarsa. Allah ba Ya kãma mutum da abin da ba ya a cikin ĩkonsa.