يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّيۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقۡتِهَآ إِلَّا هُوَۚ ثَقُلَتۡ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا تَأۡتِيكُمۡ إِلَّا بَغۡتَةٗۗ يَسۡـَٔلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنۡهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ ١٨٧
Yas'alūnaka 'anis-sā'ati ayyāna mursāhā qul innamā 'ilmuhā 'inda rabbī lā yujallīhā liwaqtihā illā huwa thaqulat fis-samāwāti wal-ardi lā ta'tīkum illā baghtatan yas'alūnaka ka annaka hafiyyun 'anhā qul innamā 'ilmuhā 'indallāhi walākinna aktharan-nāsi lā ya'lamūn
Sunã tambayar ka1 daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."
Bayanan ƙasa
1 Tambayar abin da Allah bai bayyana shi ba, kamar Rãnar Tãshin Kiyãma, yãƙi ne a tsakanin ƙarya da gaskiya. cewa wani mutum yã san gaibi ko yanã iya kãwo alheri kõ ya tunkuɗe wani sharri, ƙarya ne, kuma faɗã da gaskiya ne.