Surat Al-A'raf, aya ta 163

7:163

وَسۡـَٔلۡهُمۡ عَنِ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَتۡ حَاضِرَةَ ٱلۡبَحۡرِ إِذۡ يَعۡدُونَ فِي ٱلسَّبۡتِ إِذۡ تَأۡتِيهِمۡ حِيتَانُهُمۡ يَوۡمَ سَبۡتِهِمۡ شُرَّعٗا وَيَوۡمَ لَا يَسۡبِتُونَ لَا تَأۡتِيهِمۡۚ كَذَٰلِكَ نَبۡلُوهُم بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ ١٦٣

Was'alhum 'anil-qaryatil-latī kānat hādiratal-bahri idh ya'dūna fis-sabti idh ta'tīhim hītānuhum yawma sabtihim shurra'an wayawma lā yasbitūna lā ta'tīhim kadhālika nablūhum bimā kānū yafsuqūn

Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar1 ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.

Bayanan ƙasa

1 Wata alƙarya anã ce da ita Ailata a bãkin gãɓar Bahr Al Kulzum a zãmanin Dãwũda, Allah ya umurce su a kan harshen Dãwũda su riƙi Jumma'a rãnar ĩdi, su yanke aiki a ciki, dõmin ibãda, sai suka ƙi Jumma'a suka zãɓi Asabar, ma'anarsa yankewa. To, sai Allah ya tsananta musu, Ya hana su farautar kĩfi a rãnar Asabar, Ya halatta musu shi, a sauran kwãnukan mãko. Sai a rãnar Asabar, su sãmi kĩfi wani kan wani, amma sauran kwanuka bã su sãmunsa haka. Sai Iblis ya sanar da su ga su aikata matarar ruwa a gefen tekun, a rãnar Asabar, su bũde kifi ya shiga su rufe, har rãnar Lahadi su kãma. Sai garin ya kasu uku: kashi ɗaya suka yi farauta, wasu suka hana, sũ kuma suka yi gãru a tsakãninsu da mãsu yi, na uku ba su yi farautar ba kuma ba su hana ba. A bãyan 'yan kwãnaki sai aka mayar da mãsu farautar birai, sa'an nan suka mutu.