Surat Al-A'raf, aya ta 142

7:142

۞ وَوَٰعَدۡنَا مُوسَىٰ ثَلَٰثِينَ لَيۡلَةٗ وَأَتۡمَمۡنَٰهَا بِعَشۡرٖ فَتَمَّ مِيقَٰتُ رَبِّهِۦٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَٰرُونَ ٱخۡلُفۡنِي فِي قَوۡمِي وَأَصۡلِحۡ وَلَا تَتَّبِعۡ سَبِيلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ ١٤٢

Wawā'adnā mūsā thalāthīna laylatan wa atmamnāhā bi'ashrin fatamma mīqātu rabbihī arba'īna laylatan waqāla mūsā li akhīhi hārūnakhlufnī fī qawmī wa aslih walā tattabi' sabīlal-mufsidīn

Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin1 kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi."

Bayanan ƙasa

1 Ƙissõshin da ke tafe daga nan, suna nũna hani ga a ƙãra wani abu a cikin umarnin Allah. Kõwane irin ƙãri shi ne ake cewa bidi' a, kuma kõ dã an yi shi ne da nufin ƙwarai. Bidi'a tanã kãwo fitina ga mãsu ita.