قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱللَّهِ وَٱصۡبِرُوٓاْۖ إِنَّ ٱلۡأَرۡضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِينَ ١٢٨
Qāla mūsā liqawmihista'īnū billāhi wasbirū innal-arda lillāhi yūrithuhā man yashā'u min 'ibādihī wal-'āqibatu lil-muttaqīn
Mũsã ya ce wa mutãnensa:1 "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce."
Bayanan ƙasa
1 Maganar Mũsã ga Banĩ Isrã'ila tã nũna cewa sun ga azãbar ta yi musu yawa, har sun fãra zargin Mũsã da cewa ya sabbaba musu tsananin fitinar, da zõwarsa. Shi kuma ya lallãshe su da cewa, "Kõme ya yi tsanani, to, sauƙin sa ya yi kusa.".