Surat Al-Anbiya, aya ta 80

21:80

وَعَلَّمۡنَٰهُ صَنۡعَةَ لَبُوسٖ لَّكُمۡ لِتُحۡصِنَكُم مِّنۢ بَأۡسِكُمۡۖ فَهَلۡ أَنتُمۡ شَٰكِرُونَ ٨٠

Wa'allamnāhu san'ata labūsil lakum lituhsinakum mim ba sikum fahal antum shākirūn

Kuma Muka sanar da shi sana'ar1 wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?

Bayanan ƙasa

1 Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin neman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi.