Surat Al-An'am, aya ta 133

6:133

وَرَبُّكَ ٱلۡغَنِيُّ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفۡ مِنۢ بَعۡدِكُم مَّا يَشَآءُ كَمَآ أَنشَأَكُم مِّن ذُرِّيَّةِ قَوۡمٍ ءَاخَرِينَ ١٣٣

Warabbukal-ghaniyyu dhur-rahmati in yasha' yudhhibkum wayastakhlif mim ba'dikum mā yashā'u kamā ansha'akum min dhurriyyati qawmin ākharīn

Kuma Ubangijinika Wadãtacce1 ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.

Bayanan ƙasa

1 Rashin gaugãwar yin sãkamako ga mãsu laifi sabõda wadãtar Allah ne. Bã shi yin uƙũba dõmin Ya yi fushin an rage masa mulki, haka kuma bã shi yin ni'ima domin an ƙãra masa mulki. Sai dai dõmin Ya nũna ãdalci da falala ne kawai.