قَالُواْ يَٰٓأَبَانَا ٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَآ إِنَّا كُنَّا خَٰطِـِٔينَ ٩٧
Qālū yā'abānastaghfir lanā dhunūbanā innā kunnā khāti'īn
Suka ce: "Yã ubanmu!1 ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure."
Bayanan ƙasa
1 Ɗiyan Yãƙũbu sunã iƙrãri da laifinsu, sunã neman Allah Ya gãfarta musu gaba ɗaya. Ubansu yanã jinkirta nema musu gãfara gun Allah har a lõkacin asuba kõ kuwa daren Jumma'a dõmin ya yi rõƙo a lõkacin karɓar addu'a. Wannan yã nũna anã iya neman mai albarka kõ wani mutum yayi wa wani mutum Addu'a.