Surat Taha, aya ta 83

20:83

۞ وَمَآ أَعۡجَلَكَ عَن قَوۡمِكَ يَٰمُوسَىٰ ٨٣

Wamā a'jalaka 'an qawmika yāmūsā

"Kuma mẽne ne ya gaggautar1 da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!"

Bayanan ƙasa

1 Mũsã ya zãɓi mutun sabã'in daga Banĩ Isrã'ĩla, dõmin su tafi wurin Mĩƙãti tãre, su ji maganar Ubangiji. A lõkacin da ya yi kusa, sai ya yi gaggãwa dõmin bege. Kõ kuwa a bãyan azumin kwãna arba'in ya tafi a wurin Mĩƙãtin, Allah Ya fãra yi masa magana game da mutãnensa dõmin ɗebe masa kewa. Sai ya karɓa da cewa, "Sunã nan a kan sãwũna." Wãtau sunã nan a kan abin da na ɗõra su a kansa na addini da aƙĩda ta tauhĩdi. Sai Allah Ya ce masa "A'aha! sun musanya addininka da bautar maraƙi.".