قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّؤُاْ عَلَيۡهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِي وَلِيَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخۡرَىٰ ١٨
Qāla hiya 'asāya atawakka'u 'alayhā wa ahusshu bihā 'alā ghanamī waliya fīhā ma'āribu ukhrā
Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci1 na dabam a gare ta."
Bayanan ƙasa
1 Amfãnõnin sanda: Anã riƙon alkĩbla a cikin daji ta zama sitra, anã dõgara a kanta sabõda gajiya kõ rauni. Lĩmãmin Juma'a na dõgara a kanta a lõkacin huɗuba anã fita da ita a cikin ruwan sama anã dõgara a kanta, anã dũkan iyãli da ita dõmin ladabtarwa. A cikin wani Hadĩsi Annabi ya ce: "Ka rãtaye sandarka inda iyãlinka suke ganin ta." Riƙon sanda na sanya farkawa gabarin dũniya, watau mai ita ya zama a cikin hãlin tafiya.