إِذۡ أَوَى ٱلۡفِتۡيَةُ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ فَقَالُواْ رَبَّنَآ ءَاتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحۡمَةٗ وَهَيِّئۡ لَنَا مِنۡ أَمۡرِنَا رَشَدٗا ١٠
Idh awal-fityatu ilal-kahfi faqālū rabbanā ātinā mil ladunka rahmatan wahayyi' lanā min amrinā rashadā
A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu1! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu."
Bayanan ƙasa
1 Sun fara da addu'a ta nħman shiriya daga Allah, Ubangijinsu. Addu'a tun farko ga kõme ladabi ne. Kuma fãrãwa da nũna bautarsu ga Ubangiji, ladabi ne. Hijira da addini 1adabi ne, kuma amincewa da sãmun rahamar Allah, ladabi ne ga Allah, sabõda haka Allah ya jiɓinci tsaron kõgon ya zame musu mafi kyawun wurin zama.