وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ ٣٦
Wa innallāha rabbī warabbukum fa'budūhu hādhā sirātum mustaqīm
"Kuma lalle Allah ne Ubangijina1 kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
Bayanan ƙasa
1 Tana a cikin maganar Ĩsã a lõkacin da ya girma yana wa'azi ga mutãnensa, sabõda haka aka raba ta da maganar farko a lõkacin da yake jãrĩri.